Tsohon Alkawari

Sabon Wasiya

2 Sar 19:3-10 Littafi Mai Tsarki (HAU)

3. su ce masa, “Hezekiya ya ce, yau ranar wahala ce, da ta cin mutunci, da ta shan kunya, ga shi, 'ya'ya suna gab da a haife su, amma ba ƙarfin da za a yi yunƙuri a haife su.

4. Mai yiwuwa ne Ubangiji Allahnka ya ji dukan maganganun da Rabshake ya yi wanda ubangidansa, Sarkin Assuriya, ya aiko don yi wa Allah mai rai ba'a. Bari Ubangiji Allahnka ya hukunta masa saboda maganganunsa, sai ka yi addu'a saboda sauran da suka ragu.”

5. Sa'ad da fādawan sarki Hezekiya suka iso wurin Ishaya,

6. sai ya aike da amsa, ya ce musu, “Ku faɗa wa ubangidanku, Ubangiji ya ce, ‘Kada ka ji tsoron maganganun da ka ji daga bakin barorin Sarkin Assuriya, waɗanda suka saɓe ni.

7. Ga shi, zan sa wani ruhu a cikinsa da zai ji jita-jita, har ya koma ƙasarsa, zan sa a kashe shi da takobi a ƙasarsa.’ ”

8. Rabshake kuwa ya koma, ya tarar Sarkin Assuriya yana yaƙi da Libna, gama ya ji labari sarki ya riga ya bar Lakish.

9. Da sarki ya ji labari Tirhaka, Sarkin Habasha, ya fito don ya yi yaƙi da shi, sai ya sāke aikar manzanni wurin Hezekiya, ya ce,

10. “Ku faɗa wa Hezekiya Sarkin Yahuza, kada ya yarda Allahnsa wanda yake dogara gare shi ya yaudare shi da yi masa alkawari, cewa Sarkin Assuriya ba zai ci Urushalima ba.

Karanta cikakken babi 2 Sar 19