Tsohon Alkawari

Sabon Wasiya

2 Sar 18:33-37 Littafi Mai Tsarki (HAU)

33. Ko akwai wani allah daga cikin allolin al'ummai, wanda ya taɓa ceton ƙasarsa daga hannun Sarkin Assuriya?

34. Ina allolin Hamat, da na Arfad, da na Sefarwayim, da na Hena, da na Iwwa? Sun ceci Samariya daga hannuna ne?

35. Daga cikin dukan allolin ƙasashe, wane ne ya taɓa ceton ƙasarsa daga hannuna har da Ubangiji zai ceci Urushalima daga hannuna?’ ”

36. Sai mutanen suka yi tsit, ba wanda ya ce masa uffan, gama sarki ya umarta cewa kada a tanka masa.

37. Sa'an nan Eliyakim ɗan Hilkiya, wanda yake wakilin gidan sarki, da Shebna magatakarda, da Yowa ɗan Asaf marubuci, suka zo wurin Hezekiya da tufafinsu ketattu, suka faɗa masa irin maganar da Rabshake ya yi.

Karanta cikakken babi 2 Sar 18