Tsohon Alkawari

Sabon Wasiya

2 Sar 18:30-36 Littafi Mai Tsarki (HAU)

30. Kada kuma ku yarda Hezekiya ya sa ku dogara ga Ubangiji da cewa lalle Ubangiji zai cece ku, ba za a kuma ba da wannan birni a hannun Assuriya ba.’

31. Kada ku kasa kunne ga Hezekiya, gama Sarkin Assuriya ya ce, ‘Ku yi amana da ni, ku fito zuwa wurina. Kowane ɗayanku kuwa zai ci 'ya'yan inabinsa da 'ya'yan ɓaurensa, ya kuma sha ruwa daga cikin randarsa,

32. har lokacin da zan zo in kwashe ku, in kai ku wata ƙasa mai kama da taku, ƙasa mai yalwar hatsi, da ruwan inabi,da abinci, da gonakin inabi, da itatuwan zaitun, da zuma, don ku rayu, kada ku mutu! Kada kuma ku yarda Hezekiya ya yaudare ku da cewa Ubangiji zai cece ku.

33. Ko akwai wani allah daga cikin allolin al'ummai, wanda ya taɓa ceton ƙasarsa daga hannun Sarkin Assuriya?

34. Ina allolin Hamat, da na Arfad, da na Sefarwayim, da na Hena, da na Iwwa? Sun ceci Samariya daga hannuna ne?

35. Daga cikin dukan allolin ƙasashe, wane ne ya taɓa ceton ƙasarsa daga hannuna har da Ubangiji zai ceci Urushalima daga hannuna?’ ”

36. Sai mutanen suka yi tsit, ba wanda ya ce masa uffan, gama sarki ya umarta cewa kada a tanka masa.

Karanta cikakken babi 2 Sar 18