Tsohon Alkawari

Sabon Wasiya

2 Sar 17:18-27 Littafi Mai Tsarki (HAU)

18. Saboda wannan Ubangiji ya husata da jama'ar Isra'ila, ya kawar da su daga gabansa, ba wanda aka rage, sai dai kabilar Yahuza.

19. Jama'ar Yahuza kuma ba su kiyaye umarnan Ubangiji Allahnsu ba, sai suka bi al'adun da mutanen Isra'ila suka kawo.

20. Ubangiji kuwa ya ƙi dukan zuriyar Isra'ila, ya wahalshe su, ya kuma bashe su a hannun mugayen abokan gāba, ta haka ya kawar da su daga gabansa.

21. Sa'ad da Ubangiji ya ɓalle Isra'ila daga gidan Dawuda, sai suka naɗa Yerobowam ɗan Nebat ya zama sarki. Yerobowam kuwa ya karkatar da jama'ar Isra'ila daga bin Ubangiji. Ya sa su suka aikata babban zunubi.

22. Jama'ar Isra'ila suka yi ta aikata dukan zunuban da Yerobowam ya yi, ba su daina aikata su ba.

23. har lokacin da Ubangiji ya kawar da su daga gabansa kamar yadda ya faɗa ta bakin bayinsa, annabawa. Saboda haka aka fitar da jama'ar Isra'ila daga ƙasarsu zuwa Assuriya har wa yau.

24. Sarkin Assuriya kuwa ya kawo mutane daga Babila, da Kuta, da Awwa, da Hamat, da Sefarwayim, ya zaunar da su a garuruwan Samariya a maimakon jama'ar Isra'ila. Sai suka mallaki Samariya, suka zauna a garuruwanta.

25. A farkon zamansu a can, ba su yi tsoron Ubangiji ba saboda haka Ubangiji ya aika da zakoki a cikinsu, suka karkashe waɗansu daga cikinsu.

26. Sai aka faɗa wa Sarkin Assuriya cewa, “Al'umman da ka kwashe ka zaunar da su a garuruwan Samariya ba su san shari'ar Allahn ƙasar ba, domin haka ya aiki zakoki a cikinsu, suna ta karkashe su.”

27. Sa'an nan Sarkin Assuriya ya umarta a aiki firist ɗaya daga cikin firistocin da aka kwashe daga can, ya tafi, ya zauna can domin ya koya musu shari'ar Allahn ƙasar.

Karanta cikakken babi 2 Sar 17