Tsohon Alkawari

Sabon Wasiya

2 Sar 14:25-29 Littafi Mai Tsarki (HAU)

25. Ya kafa iyakar Isra'ila daga ƙofar Hamat har zuwa tekun Araba. Wannan kuwa shi ne abin da Ubangiji, Allah na Isra'ila, ya faɗa ta bakin bawansa annabi Yunana, ɗan amittai, daga Gathefer.

26. Gama Ubangiji ya ga Isra'ila tana shan azaba mai tsanani, gama ba bawa ko ɗa wanda zai taimaki Isra'ila.

27. Ubangiji kuwa bai ce zai shafe sunan Isra'ila daga duniya ba, saboda haka ya cece su ta hannun Yerobowam na biyu.

28. Sauran ayyukan Yerobowam na biyu, da dukan abin da ya yi, da ƙarfinsa, da yaƙi da ya yi, da yadda ya ƙwato wa Isra'ila Dimashƙu da Hamat waɗanda suke na Yahuza, an rubuta su a littafin tarihin sarakunan Isra'ila.

29. Yerobowam na biyu kuwa ya mutu, kamar kakanninsa, sarakunan Isra'ila. Zakariya ɗansa ya gaji sarautarsa.

Karanta cikakken babi 2 Sar 14