Tsohon Alkawari

Sabon Wasiya

2 Sar 13:13-20 Littafi Mai Tsarki (HAU)

13. Yehowash kuwa ya mutu, aka binne shi a Samariya, inda ake binne sarakunan Isra'ila, sai Yerobowam na biyu ya gāji gadon sarautarsa.

14. Da Elisha ya kamu da ciwon ajali, sai Yehowash Sarkin Isra'ila ya tafi wurinsa, ya yi kuka a gabansa, yana cewa, “Ubana, Ubana, karusar Isra'ila da mahayan dawakanta!”

15. Elisha kuwa ya ce masa, “Ka ɗauki baka da kibau.” Shi kuwa ya ɗauka.

16-17. Sa'an nan ya ce, “Ka buɗe tagar da take wajen gabas.” Sai ya buɗe. Elisha ya kuma ce masa, “Ka ja bakan.” Ya kuwa ja. Sai Elisha ya ɗora hannuwansa a bisa hannuwan sarki. Sa'an nan Elisha ya ce, “Harba.” Sai ya harba. Elisha kuwa ya ce, “Kibiyar Ubangiji ta nasara, kibiyar nasara a kan Suriya. Gama za ka yi yaƙi da Suriyawa a Afek har ka ci su.”

18. Sa'an nan ya ce, “Ka ɗauki kibau.” Shi kuwa ya ɗauka. Sai ya ce wa Sarkin Isra'ila, “Ka caki ƙasa da su.” Sai ya caka har sau uku, sa'an nan ya tsaya.

19. Elisha kuwa ya husata, ya ce, “Da ma ka caka sau biyar ko shida da za ka yi nasara a kan Suriyawa har ka ci su sarai, amma yanzu za ka yi nasara da su sau uku kawai.”

20. Elisha kuwa ya rasu, aka binne shi.Maharan Mowabawa sukan kawo yaƙi a ƙasar da bazara.

Karanta cikakken babi 2 Sar 13