Tsohon Alkawari

Sabon Wasiya

2 Sar 10:21-36 Littafi Mai Tsarki (HAU)

21. sai ya aika cikin Isra'ila duka, dukan masu yi wa Ba'al sujada kuwa suka zo, ba wanda bai zo ba. Suka shiga, suka cika haikalin Ba'al makil daga wannan gefe zuwa wancan.

22. Sa'an nan Yehu ya ce wa wanda yake lura da ɗakin tufafi, “Ku fito da tufafi na dukan waɗanda suke yi wa Ba'al sujada.” Shi kuwa ya fito musu da tufafin.

23. Bayan wannan Yehu ya shiga haikalin Ba'al tare da Yehonadab ɗan Rekab, ya ce wa masu yi wa Ba'al sujada, “Ku bincike, ku tabbata, ba wani bawan Ubangiji tare da ku, sai dai masu yi wa Ba'al sujada kaɗai.”

24. Sa'an nan Yehu da Yehonadab suka shiga don su miƙa sadaka da hadayu na ƙonawa. Yehu ya riga ya sa mutum tamanin a waje, ya ce musu, “Mutumin da ya bar wani daga cikin waɗanda na bashe su a hannunku ya tsere, to, a bakin ransa.”

25. Nan da nan da Yehu ya gama miƙa hadaya ta ƙonawa, sai ya ce wa mai tsaro da shugabannin, “Ku shiga, ku karkashe su, kada ku bar wani ya tsere.” Da suka karkashe su, sai suka fitar da su waje, sa'an nan suka shiga can cikin haikalin Ba'al.

26. Suka fitar da gumakan da suke cikin haikalin Ba'al, suka ƙone su.

27. Suka yi kaca kaca da gunkin Ba'al da haikalinsa, suka mai da haikalin ya zama salga har wa yau.

28. Yehu ya kawar da Ba'al daga cikin Isra'ila.

29. Amma bai rabu da zunubin Yerobowam ɗan Nebat ba, wanda ya sa Isra'ila su yi zunubi. Siffofin maruƙa biyu suna nan a Betel da Dan.

30. Ubangiji kuwa ya ce wa Yehu, “Da yake ka yi abin da yake daidai a gare ni, ka yi wa gidan ahab bisa ga dukan abin da yake a zuciyata, 'ya'yanka, har tsara ta huɗu, za su ci sarautar Isra'ila.”

31. Amma Yehu bai mai da hankali ya yi tafiya a tafarkin Ubangiji Allah na Isra'ila da zuciya ɗaya ba. Bai rabu da zunuban Yerobowam ba, wanda ya sa Isra'ila su yi zunubi.

32. A kwanakin an Ubangiji ya soma rage ƙasar Isra'ila. Hazayel kuwa ya yaƙe su a karkarar Isra'ila,

33. tun daga Urdun har zuwa wajen gabas, da dukan ƙasar Gileyad, da ta Gad, da ta Ra'ubainu, da ta Manassa, tun daga Arower wadda dake kusa da kwarin Arnon haɗe da Gileyad da Bashan.

34. Sauran ayyukan Yehu da dukan abin da ya yi, da dukan ƙarfinsa an rubuta su a littafin tarihin sarakuna Isra'ila.

35. Yehu kuwa ya rasu, aka binne shi a Samariya. Yehowahaz ɗansa ya gaji sarautarsa.

36. Yehu ya yi mulkin Isra'ila a Samariya shekara ashirin da takwas.

Karanta cikakken babi 2 Sar 10