Tsohon Alkawari

Sabon Wasiya

2 Sam 8:5-18 Littafi Mai Tsarki (HAU)

5. Suriyawan Dimashƙu kuwa, suka zo don su taimaki Hadadezer, Sarkin Zoba, Dawuda kuwa ya kashe Suriyawa dubu ashirin da dubu biyu (22,000).

6. Sa'an nan ya ajiye ƙungiyoyin sojojinsa a Suriya ta Dimashƙu. Suriyawa suka zama talakawan Dawuda, suka riƙa kawo masa haraji. Duk inda Dawuda ya tafi, Ubangiji yakan taimake shi.

7. Dawuda ya kwashe garkuwoyi na zinariya waɗanda shugabannin sojojin Hadadezer suka riƙe, ya kawo su Urushalima.

8. Ya kuma kwashe tagulla da yawa daga Beta da Berotayi biranen Hadadezer.

9. Sa'ad da Toyi Sarkin Hamat ya ji labari Dawuda ya ci dukan rundunar Hadadezer da yaƙi,

10. sai ya aiki Adoniram ɗansa wurin sarki Dawuda don ya gaishe shi, ya kuma yaba masa saboda ya ci Hadadezer da yaƙi, gama Hadadezer yakan yi yaƙi da Toyi kullum. Adoniram kuwa ya kawo wa Dawuda kyautar kayan azurfa, da na zinariya, da na tagulla.

11. Dawuda ya keɓe wa Ubangiji kayayyakin nan tare da azurfa da zinariya da ya karɓe daga dukan al'umman da ya mallaka,

12. wato azurfa da zinariya na Edomawa, da na Mowabawa, da na Ammonawa, da na Filistiyawa, da na Amalekawa, da ganimar Hadadezer ɗan Rehob, Sarkin Zoba.

13. Dawuda kuwa ya yi suna. Ya kashe Edomawa dubu goma sha takwas (18,000) a kwarin Gishiri sa'ad da yake komowa.

14. Sai ya sa ƙungiyoyin sojoji a ƙasar Edom duka. Edomawa suka zama talakawan Dawuda. Ubangiji ya ba Dawuda nasara duk inda ya tafi.

15. Dawuda ya mallaki Isra'ila duka. Ya yi wa dukan jama'arsa shari'ar gaskiya da adalci.

16. Yowab ɗan Zeruya, shi ne shugaban sojojin. Yehoshafat ɗan Ahilud, shi ne marubuci.

17. Zadok ɗan Ahitub, da Ahimelek ɗan Abiyata, su ne firistoci. Seraiya shi ne magatakarda.

18. Benaiya ɗan Yehoyada, shi ne shugaban Keretiyawa da Feletiyawa, wato matsara. 'Yan'yan Dawuda, maza, suka zama mataimakansa.

Karanta cikakken babi 2 Sam 8