Tsohon Alkawari

Sabon Wasiya

2 Sam 8:4-14 Littafi Mai Tsarki (HAU)

4. Dawuda ya ƙwace masa mahayan dawakai dubu ɗaya da ɗari bakwai (1,700), da sojojin ƙafa dubu ashirin (20,000). Dawuda ya yanyanke agarar dawakan, sai dai doki ɗari ne ya bari.

5. Suriyawan Dimashƙu kuwa, suka zo don su taimaki Hadadezer, Sarkin Zoba, Dawuda kuwa ya kashe Suriyawa dubu ashirin da dubu biyu (22,000).

6. Sa'an nan ya ajiye ƙungiyoyin sojojinsa a Suriya ta Dimashƙu. Suriyawa suka zama talakawan Dawuda, suka riƙa kawo masa haraji. Duk inda Dawuda ya tafi, Ubangiji yakan taimake shi.

7. Dawuda ya kwashe garkuwoyi na zinariya waɗanda shugabannin sojojin Hadadezer suka riƙe, ya kawo su Urushalima.

8. Ya kuma kwashe tagulla da yawa daga Beta da Berotayi biranen Hadadezer.

9. Sa'ad da Toyi Sarkin Hamat ya ji labari Dawuda ya ci dukan rundunar Hadadezer da yaƙi,

10. sai ya aiki Adoniram ɗansa wurin sarki Dawuda don ya gaishe shi, ya kuma yaba masa saboda ya ci Hadadezer da yaƙi, gama Hadadezer yakan yi yaƙi da Toyi kullum. Adoniram kuwa ya kawo wa Dawuda kyautar kayan azurfa, da na zinariya, da na tagulla.

11. Dawuda ya keɓe wa Ubangiji kayayyakin nan tare da azurfa da zinariya da ya karɓe daga dukan al'umman da ya mallaka,

12. wato azurfa da zinariya na Edomawa, da na Mowabawa, da na Ammonawa, da na Filistiyawa, da na Amalekawa, da ganimar Hadadezer ɗan Rehob, Sarkin Zoba.

13. Dawuda kuwa ya yi suna. Ya kashe Edomawa dubu goma sha takwas (18,000) a kwarin Gishiri sa'ad da yake komowa.

14. Sai ya sa ƙungiyoyin sojoji a ƙasar Edom duka. Edomawa suka zama talakawan Dawuda. Ubangiji ya ba Dawuda nasara duk inda ya tafi.

Karanta cikakken babi 2 Sam 8