Tsohon Alkawari

Sabon Wasiya

2 Sam 8:3-10 Littafi Mai Tsarki (HAU)

3. Dawuda kuma ya ci Hadadezer ɗan Rehob, Sarkin Zoba, da yaƙi lokacin da shi Hadadezer yake kan tafiya zuwa Kogin Yufiretis don ya tabbatar da ikonsa a wurin.

4. Dawuda ya ƙwace masa mahayan dawakai dubu ɗaya da ɗari bakwai (1,700), da sojojin ƙafa dubu ashirin (20,000). Dawuda ya yanyanke agarar dawakan, sai dai doki ɗari ne ya bari.

5. Suriyawan Dimashƙu kuwa, suka zo don su taimaki Hadadezer, Sarkin Zoba, Dawuda kuwa ya kashe Suriyawa dubu ashirin da dubu biyu (22,000).

6. Sa'an nan ya ajiye ƙungiyoyin sojojinsa a Suriya ta Dimashƙu. Suriyawa suka zama talakawan Dawuda, suka riƙa kawo masa haraji. Duk inda Dawuda ya tafi, Ubangiji yakan taimake shi.

7. Dawuda ya kwashe garkuwoyi na zinariya waɗanda shugabannin sojojin Hadadezer suka riƙe, ya kawo su Urushalima.

8. Ya kuma kwashe tagulla da yawa daga Beta da Berotayi biranen Hadadezer.

9. Sa'ad da Toyi Sarkin Hamat ya ji labari Dawuda ya ci dukan rundunar Hadadezer da yaƙi,

10. sai ya aiki Adoniram ɗansa wurin sarki Dawuda don ya gaishe shi, ya kuma yaba masa saboda ya ci Hadadezer da yaƙi, gama Hadadezer yakan yi yaƙi da Toyi kullum. Adoniram kuwa ya kawo wa Dawuda kyautar kayan azurfa, da na zinariya, da na tagulla.

Karanta cikakken babi 2 Sam 8