An kuma yi wani yaƙi a Gat, inda aka sami wani ƙaton mutum wanda shi cindo ne, hannuwa da ƙafafu, wato yana da yatsotsi ashirin da huɗu ke nan. Shi kuma daga cikin zuriyar gwarzayen mutanen ne.