Tsohon Alkawari

Sabon Wasiya

2 Sam 20:16-26 Littafi Mai Tsarki (HAU)

16. Sai wata mace mai hikima ta yi kira daga cikin garin, ta ce, “Ji mana! A faɗa wa Yowab, ya zo nan, ina so in yi magana da shi.”

17. Da ya zo kusa da ita, sai macen ta ce, “Kai ne Yowab?”Ya ce, “I, ni ne.”Ta ce masa, “Ka kasa kunne gare ni.”Ya ce, “Ina sauraronki.”

18. Ta ce, “A dā sukan ce, ‘A nemi shawara a Abel,’ gama a can ake raba gardama.

19. Garinmu lafiyayye ne, amintacce ne kuma a cikin Isra'ila. Me ya sa kake so ka hallaka garin? Kana so ka rushe abin da yake na Allah?”

20. Yowab ya ce, “Allah ya sawwaƙe! Ba zan lalatar ko in hallakar da birninku ba.

21. Ba haka ba ne, ni dai ina neman mutumin ƙasar tudu ta Ifraimu, wanda ake ce da shi Sheba, ɗan Bikri. Shi ne ya tayar wa sarki Dawuda. Shi kaɗai za ku ba ni, ni kuwa zan janye daga garin.”Macen kuwa ta ce wa Yowab, “To, za a jefar maka kansa ta kan garu.”

22. Macen ta tafi wurin dukan mutanen garin da wayo. Su kuwa suka yanke kan Sheba, ɗan Bikri, suka jefa wa Yowab. Sa'an nan Yowab ya busa ƙaho, suka janye daga garin. Kowa ya tafi gidansa. Yowab kuma ya koma Urushalima wurin sarki.

23. Yowab shi ne shugaban dukan sojojin Isra'ila, Benaiya, ɗan Yehoyada shi ne shugaban Keretiyawa da Feletiyawa, wato masu tsaro.

24. Adoniram shi ne shugaban aikin gandu, Yehoshafat, ɗan Ahilud, shi ne marubuci.

25. Shewa shi ne magatakarda. Zadok da Abiyata su ne firistoci.

26. Aira mutumin Yayir shi ne mashawarcin Dawuda.

Karanta cikakken babi 2 Sam 20