Tsohon Alkawari

Sabon Wasiya

2 Sam 2:22-32 Littafi Mai Tsarki (HAU)

22. Abner kuma ya sāke ce masa, “Ka daina bina, kada ka sa in kashe ka fa! Idan na kashe ka kuwa, yaya zan yi ido biyu da dan'uwanka, Yowab?”

23. Amma Asahel bai daina binsa ba, Abner dai ya nashe shi da gindin māshi a ciki, sai mashin ya fita ta bayansa. Ya fāɗi ya mutu nan take. Duk wanda ya zo inda Asahel ya fāɗi ya mutu, sai ya tsaya cik.

24. Amma Yowab da Abishai suka bi Abner, har faɗuwar rana, suka isa tudun Amma, wanda yake gaban Gaiya, a hanya zuwa jejin Gibeyon.

25. Mutanen Biliyaminu kuma suka haɗa kansu, suka goyi bayan Abner, suka zama ƙungiya guda, suka tsaya kan tudu.

26. Abner kuwa ya kira Yowab, ya ce, “Har abada ne takobi zai hallakar? Ba ka sani ba ƙarshen zai yi ɗaci? Sai yaushe za ka umarci mutanenka su daina runtumar 'yan'uwansu?”

27. Yowab ya ce, “Na rantse da Ubangiji, hakika da ba domin ka yi magana ba, da mutanena ba za su daina runtumarka ba har gobe da safe.”

28. Sa'an nan Yowab ya busa ƙaho, dukan mutanensa kuwa suka tsaya, ba su ƙara runtumar mutanen Isra'ila ba, ba wanda kuma ya yaƙi wani.

29. Abner da mutanensa suka bi dare farai, suka ratsa Araba, suka haye Urdun. Suka yi ta tafiya dukan safiyan nan, suka shige Bitron, har suka kai Mahanayim.

30. Da Yowab ya komo daga runtumar Abner, ya tattara mutanensa duka, sai ya ga an rasa mutum goma sha tara daga cikin mutanen Dawuda, banda Asahel.

31. Amma barorin Dawuda suka kashe mutanen Biliyaminu mutum ɗari uku da sittin daga cikin waɗanda suke tare da Abner.

32. Suka ɗauki Asahel, suka tafi suka binne shi a kabarin mahaifinsa a Baitalami. Yowab kuwa da mutanensa suka bi dare farai, gari ya waye musu a Hebron.

Karanta cikakken babi 2 Sam 2