Tsohon Alkawari

Sabon Wasiya

2 Sam 16:13-23 Littafi Mai Tsarki (HAU)

13. Dawuda da mutanensa suka ci gaba da tafiyarsu. Shimai kuwa yana biye da su ta gefen dutse, yana tafe, yana ta zagi, yana jifarsa da duwatsu, yana masa ature.

14. Sarki da dukan jama'ar da suke tare da shi suka isa Urdun a rafke. Sai suka shaƙata.

15. Absalom kuwa ya zo Urushalima tare da dukan mutanen Isra'ila da suke tare da shi. Ahitofel kuma yana tare da shi.

16. Sa'ad da Hushai Ba'arkite, aminin Dawuda ya zo wurin Absalom, ya ce masa, “Ran sarki ya daɗe!”

17. Sai Absalom ya ce wa Hushai, “Ƙaunar da kake yi wa abokinka ke nan? Me ya sa ba ka tafi tare da abokinka ba?”

18. Hushai ya amsa, ya ce, “Ba haka ba, ni dai zan zama na wanda Ubangiji, da wannan jama'a, dukan mutanen Isra'ila suka zaɓa. Zan zauna tare da mutumin da aka zaɓa.

19. Banda haka ma, wane ne ya kamata in bauta wa, in ba ɗan ubangidana ba? Kamar yadda na bauta wa tsohonka, haka kuma zan bauta maka.”

20. Sa'an nan Absalom ya juya wajen Ahitofel, ya ce, “To, ka kawo shawararka a kan abin da ya kamata mu yi?”

21. Ahitofel kuwa ya ce wa Absalom, “Ka shiga ka kwana, da ƙwarakwaran tsohonka waɗanda ya bar su su lura da gidan. Dukan Isra'ilawa za su sani ba shiri kuma tsakaninka da tsohonka. Dukan masu goyon bayanka kuma za su ƙara ƙarfafa.”

22. Sai suka kafa wa Absalom alfarwa a bisa kan soro, ya shiga ya kwana da ƙwaraƙwaran tsohonsa, a idon mutanen Isra'ila duka.

23. Shawarar da Ahitofel yake bayarwa a lokacin nan ta zama kamar faɗar Allah ce. Absalom duk da Dawuda, shawarar Ahitofel suke bi.

Karanta cikakken babi 2 Sam 16