Tsohon Alkawari

Sabon Wasiya

2 Sam 14:7-15 Littafi Mai Tsarki (HAU)

7. Yanzu kuwa dukan dangi sun tasar mini, suna cewa, in ba da ɗayan wanda ya kashe ɗan'uwansa domin su kashe shi saboda ran ɗan'uwansa da ya kashe. Wato za su hallaka magāji ke nan, ta haka za a yi biyu babu ke nan, su bar mijina ba suna ko zuriya a duniya.”

8. Sarki kuwa ya ce mata, “Ki tafi gidanki, zan daidaita maganarki.”

9. Sai ta ce wa sarki, “Ya ubangijina, sarki, bari laifin ya zauna a kaina da gidan mahaifina, sarki kuwa da gadon sarautarsa ya barata.”

10. Sarki ya ce mata, “In wani ya ƙara ce miki wani abu, ki kawo shi wurina, ba zai ƙara yi miki fitina ba.”

11. Sai ta ce, “Ina roƙonka, ya sarki, ka rantse da Ubangiji Allahnka, kada a bar masu bin hakkin jini su yi ramako, don kada su kashe ɗana.”Ya ce mata, “Na rantse miki da zatin Ubangiji, ko gashin kansa guda ɗaya ba zai faɗi ƙasa ba.”

12. Ta kuma ce, “Ina roƙonka, ya ubangijina sarki, ka bar ni in yi magana.”Sai ya ce, “Yi maganarki.”

13. Sa'an nan ta ce, “To, me ya sa ka yi wa jama'ar Allah irin wannan abu? Gama bisa ga maganar bakinka, ya sarki, ka hukunta kanka tun da yake sarki bai yarda ɗansa ya komo gida ba.

14. Dukanmu mutuwa za mu yi, kamar ruwan da ya zube a ƙasa, wanda ba ya kwasuwa, haka za mu zama. Allah ba yakan ɗauke rai kurum ba, amma yakan shirya hanya domin wanda ya shuɗe ba zai ɓata daga gabansa ba.

15. Saboda mutane sun tsorata ni shi ya sa na zo in faɗa wa ubanjijina, sarki. Na kuwa yi tunani na ce, ‘Zan tafi in faɗa wa sarki, watakila sarki zai amsa roƙona.

Karanta cikakken babi 2 Sam 14