Tsohon Alkawari

Sabon Wasiya

2 Sam 14:12-25 Littafi Mai Tsarki (HAU)

12. Ta kuma ce, “Ina roƙonka, ya ubangijina sarki, ka bar ni in yi magana.”Sai ya ce, “Yi maganarki.”

13. Sa'an nan ta ce, “To, me ya sa ka yi wa jama'ar Allah irin wannan abu? Gama bisa ga maganar bakinka, ya sarki, ka hukunta kanka tun da yake sarki bai yarda ɗansa ya komo gida ba.

14. Dukanmu mutuwa za mu yi, kamar ruwan da ya zube a ƙasa, wanda ba ya kwasuwa, haka za mu zama. Allah ba yakan ɗauke rai kurum ba, amma yakan shirya hanya domin wanda ya shuɗe ba zai ɓata daga gabansa ba.

15. Saboda mutane sun tsorata ni shi ya sa na zo in faɗa wa ubanjijina, sarki. Na kuwa yi tunani na ce, ‘Zan tafi in faɗa wa sarki, watakila sarki zai amsa roƙona.

16. Gama sarki zai ji, ya cece ni daga hannun mutumin nan da zai hallaka ni tare da ɗana daga cikin jama'ar Allah.’

17. Na kuma yi tunani a kan maganar ubangijina, sarki, za ta kwantar da zuciyata, gama ubangijina, sarki, kamar mala'ikan Allah yake, yana rarrabe tsakanin nagarta da mugunta. Ubangiji Allahnka ya kasance tare da kai!”

18. Sai sarki ya ce mata, “Kada ki rufe mini duk abin da zan tambaye ki.”Ta ce, “To, ka yi tambayarka.”

19. Sa'an nan ya ce mata, “Ko akwai hannun Yowab cikin dukan sha'anin nan naki?”Ita kuwa ta amsa, “Na rantse da kai, ya ubangijina, sarki, ba dama a yi maka ƙumbiya-ƙumbiya. Haka ne, Yowab baranka ne ya sa ni. Shi ya sa dukan waɗannan magana a bakin baranyarka.

20. Yowab baranka ya yi wannan don ya daidaita al'amarin. Amma ubangijina yana da hikima irin ta mala'ikan Allah domin ya san dukan al'amuran da suke a duniya.”

21. Sa'an nan sarki ya ce wa Yowab, “To, na yarda, sai ka tafi ka komo da saurayin nan, Absalom.”

22. Sai Yowab ya rusuna har ƙasa da bangirma, ya yi wa sarki kyakkyawan fata. Ya kuma ce, “Yau na sani na sami tagomashi a wurinka, ya ubangijina, sarki, da yake ka amsa roƙona.”

23. Sa'an nan Yowab ya tashi, ya tafi Geshur, ya komo da Absalom Urushalima.

24. Sarki ya ce a sa shi ya koma gidansa, kada ya zo gabansa. Absalom kuwa ya yi zamansa can gidansa, bai je gaban sarki ba.

25. A cikin Isra'ila duka ba wanda ake yaba kyansa kamar Absalom. Tun daga tafin sawunsa har zuwa bisa kansa ba shi da makusa.

Karanta cikakken babi 2 Sam 14