Tsohon Alkawari

Sabon Wasiya

2 Sam 13:9-21 Littafi Mai Tsarki (HAU)

9. Ta juye wainar daga kaskon yana gani, amma ya ƙi ci. Ya ce wa waɗanda suke cikin ɗakin su fita. Su kuwa suka fita.

10. Sa'an nan Amnon ya ce wa Tamar, “Kawo abincin a cikin ɗakin kwanana, ki riƙe mini in ci.” Sai ta ɗauki wainar da ta yi, ta kai wa Amnon, wanta, a ɗakin kwana.

11. Amma da ta kawo kusa da shi don ya ci, ya kama ta, ya ce, “Zo in kwana da ke ƙanwata.”

12. Ta ce masa, “Haba, wana, kada ka ƙasƙantar da ni, gama ba a yin haka a cikin Isra'ila, kada ka yi halin dabba.

13. Ni kuwa ina zan sa kaina saboda kunya? Kai kuwa za ka zama ɗaya daga cikin riƙaƙƙun sakarkarin mutane na cikin Isra'ila. Ina roƙonka ka yi magana da sarki, gama ba zai hana ka ka aure ni ba.”

14. Amma Amnon bai ji maganarta ba. Da yake ya fi ta ƙarfi, sai ya yi mata faɗe.

15. Bayan haka sai Amnon ya ƙi ta da mummunar ƙiyayya, har ƙiyayyar ta fi yawan ƙaunar da ya yi mata. Ya ce mata, “Tashi, ki fita.”

16. Sai ta ce masa, “A'a wana, muguntar koran nan da kake yi mini, ta fi ta wadda ka riga ka yi mini.”Amma bai kasa kunne gare ta ba.

17. Sai ya kira baran da yake yi masa hidima, ya ce, “Fitar da matan nan daga gabana, ka rufe ƙofa.”

18. Tamar kuwa tana saye da doguwar riga mai hannuwa, gama haka gimbiyoyi budurwai suke ado. Baran Amnon kuwa ya fitar da ita, ya kulle ƙofar.

19. Tamar ta baɗe kanta da toka, ta keta doguwar rigarta mai hannuwa wadda ta sa, ta rufe fuska da hannu, ta tafi tana ta kuka da ƙarfi.

20. Absalom wanta ya tambaye ta, ya ce, “Ko Amnon wanki ya ɓata ki? To, yi shiru, ƙanwata, shi wanki ne, kada ki damu da yawa.” Tamar kuwa ta zauna a kaɗaice a gidan Absalom wanta.

21. Da Dawuda sarki ya ji wannan, sai ya husata ƙwarai.

Karanta cikakken babi 2 Sam 13