Tsohon Alkawari

Sabon Wasiya

2 Sam 13:25-37 Littafi Mai Tsarki (HAU)

25. Amma sarki ya ce wa Absalom, “A'a ɗana, ba ma tafi duka ba, don kada mu nawaita maka.” Absalom ya dāge cewa, sai sarki ya je, amma duk da haka sarki bai tafi ba, sai dai ya sa masa albarka.

26. Sa'an nan Absalom ya ce, “Idan ba za ka tafi ba, ina roƙonka ka bar Amnon ɗan'uwana ya tafi tare da mu.”Sarki ya ce, “Don me zai tafi tare da kai?”

27. Amma Absalom ya dāge har sarki ya yarda. Amnon da dukan 'ya'yan sarki suka tafi tare da shi.

28. Absalom ya umarci barorinsa, ya ce, “Ku lura sa'ad da Amnon ya bugu da ruwan inabi, in na ce, ‘Bugi Amnon’, sai ku kashe shi. Kada ku ji tsoro, gama ni na umarce ku, sai dai ku yi ƙarfin hali, ku yi jaruntaka.”

29. Haka kuwa barorin Absalom suka kashe Amnon yadda Absalom ya umarta. Sauran 'ya'yan sarki kuwa suka tashi, kowa ya hau alfadarinsa, ya gudu.

30. Sa'ad da suke kan hanya labari ya kai kunnen Dawuda. Aka ce, “Absalom ya kashe dukan 'ya'yan sarki, ba wanda ya tsira daga cikinsu.”

31. Sai sarki ya tashi ya keta rigunansa, ya kwanta a ƙasa. Dukan barorinsa kuma da suke tsaye a wurin suka kyakketa rigunansu.

32. Amma Yonadab, ɗan Shimeya, ɗan'uwan Dawuda, ya ce, “Ranka ya daɗe, ba fa dukan 'ya'yan sarki aka kashe ba. Amnon ne kaɗai aka kashe ta umarnin Absalom, gama ya ƙudura wannan tun daga ranar da Amnon ya yi wa Tamar ƙanwarsa faɗe.

33. Don haka, kada shugabana sarki ya damu, cewa, an kashe dukan 'ya'yan sarki, gama Amnon ne kaɗai aka kashe.”

34. Absalom kuwa ya gudu.Sa'an nan sojan da yake tsaro a wannan lokaci ya ga ɗumbun mutane suna tahowa daga hanyar Horonayim, wajen gefen dutse.

35. Sai Yonadab ya ce wa sarki, “Waɗannan 'ya'yan sarki ne yake zuwa, kamar yadda na faɗa.”

36. Yana gama magana ke nan, sai ga 'ya'yan sarki sun iso. Suka yi ta kuka da ƙarfi. Sarki kuma da dukan fādawansa suka yi kuka mai tsanani.

37. Amma Absalom ya gudu ya tafi wurin Talmai, ɗan Ammihud, Sarkin Geshur. Dawuda kuwa ya yi makokin Amnon ɗansa kwana da kwanaki.

Karanta cikakken babi 2 Sam 13