Tsohon Alkawari

Sabon Wasiya

2 Sam 12:24-31 Littafi Mai Tsarki (HAU)

24. Sa'an nan Dawuda ya yi wa Batsheba, matarsa, ta'aziyya. Ya shiga wurinta, ya kwana da ita. Ta haifa masa ɗa. Ya raɗa masa suna Sulemanu. Ubangiji kuwa ya ƙaunace shi,

25. ya kuma umarci annabi Natan ya raɗa wa yaron suna Yedideya, wato ƙaunataccen Ubangiji.

26. Yowab kuwa ya yi yaƙi da Rabba ta Ammonawa, yana kuwa gab da cin birnin.

27. Sai ya aiki manzanni wurin Dawuda ya ce, “Na yaƙi Rabba, na kama hanyar samun ruwansu.

28. Yanzu ka tara sauran sojoji ka fāɗa wa birnin, ka ci shi da kanka. Gama ba na so in yi suna da cin birnin.”

29. Saboda haka sai Dawuda ya tara sauran sojoji duka, ya tafi Rabba, ya yi yaƙi da ita, ya kuwa ci birnin.

30. Sarkinsu, wato Milkom, yana da kambi na zinariya a kansa, nauyinsa ya kai talanti ɗaya na zinariya yana kuma da duwatsu masu daraja cikinsa. Dawuda kuwa ya ɗauke kambin daga kan sarkin ya sa a nasa. Sa'an nan ya kwaso ganima mai ɗumbun yawa daga cikin birnin.

31. Ya kuma kamo mutanen da suke cikin birnin, ya sa su su yi aiki da zartuka, da faretani, da gatura. Ya kuma sa su yi tubula. Haka Dawuda ya yi da dukan biranen Ammonawa. Sa'an nan Dawuda da dukan sojojinsa suka koma Urushalima.

Karanta cikakken babi 2 Sam 12