Tsohon Alkawari

Sabon Wasiya

2 Sam 11:10-15 Littafi Mai Tsarki (HAU)

10. Da aka faɗa wa Dawuda, cewa, Uriya bai tafi gidansa ba, Dawuda ya kira Uriya ya ce masa, “Ka dawo daga tafiya, me ya sa ba ka tafi gidanka ba?”

11. Uriya ya ce wa Dawuda, “Akwatin alkawari, da mutanen Isra'ila, da na Yahuza, suna zaune a bukkoki. Shuganana Yowab, da barorinsa suna zaune a sansani a karkara, ƙaƙa ni zan tafi gidana in ci in sha, in kwanta da matata? Na rantse da ranka, ba zan yi haka ba.”

12. Dawuda kuma ya ce wa Uriya, “Ka kwana nan kuma yau, gobe in sallame ka.” Sai Uriya ya kwana a Urushalima a ran nan.

13. Kashegari kuma Dawuda ya kira shi liyafa. Ya zo, ya ci ya sha tare da shi, har Dawuda ya sa shi ya bugu. Amma da dare, sai ya tafi ya kwanta a shimfiɗarsa tare da sauran barorin sarki, amma bai tafi gidansa ba.

14. Da safe Dawuda ya rubuta wasiƙa, ya ba Uriya ya kai wa Yowab.

15. A wasiƙar ya ce wa Yowab, “Tura Uriya a gaba a inda yaƙin ya fi zafi, sa'an nan ku ja da baya, ku bar shi don a buge shi a kashe shi.”

Karanta cikakken babi 2 Sam 11