Tsohon Alkawari

Sabon Wasiya

2 Sam 11:1-10 Littafi Mai Tsarki (HAU)

1. Da bazara lokacin da sarakuna sukan fita zuwa yaƙi, Dawuda ya aiki Yowab, da shugabannin sojojinsa, da sojojin Isra'ila duka. Suka tafi suka ragargaza Ammonawa, suka kuma kewaya Rabba da yaƙi. Amma Dawuda ya yi zamansa a Urushalima.

2. Wata rana da yamma Dawuda ya tashi daga shaƙatawa, yana yawo a kan rufin soron fādarsa, can ya hangi wata kyakkyawar mata tana wanka.

3. Sai ya aika a bincika ko wace ce wannan mata, ashe, 'yar Ammiyel ce, matar Uriya Bahitte.

4. Dawuda kuwa ya aiki waɗansu manzanni suka kawo masa ita, ya kwana da ita. (A lokacin kuwa ta gama wankan haila ke nan.) Sa'an nan ta koma gidanta.

5. Matar kuwa ta yi juna biyu, sai ta aika a faɗa wa Dawuda, cewa, tana da ciki.

6. Dawuda kuwa ya aika wurin Yowab ya ce, “Ka aiko mini da Uriya Bahitte.” Yowab kuwa ya aika da Uriya wurin Dawuda.

7. Da Uriya ya iso, sai Dawuda ya tambaye shi labarin Yowab, da lafiyar jama'ar, da labarin yaƙin.

8. Ya kuma ce masa, “Ka tafi gidanka, ka wanke ƙafafunka.” Da Uriya ya fita daga gidan sarki, sarki ya ba da kyauta a kai masa.

9. Amma Uriya bai tafi gidansa ba, sai ya kwana a ƙofar gidan sarki tare da sauran barorin sarki.

10. Da aka faɗa wa Dawuda, cewa, Uriya bai tafi gidansa ba, Dawuda ya kira Uriya ya ce masa, “Ka dawo daga tafiya, me ya sa ba ka tafi gidanka ba?”

Karanta cikakken babi 2 Sam 11