Tsohon Alkawari

Sabon Wasiya

2 Sam 1:9-20 Littafi Mai Tsarki (HAU)

9. Sai ya ce mini, ‘Zo ka kashe ni gama ina cikin azaba, amma raina bai fita ba.’

10. Sai na tafi na kashe shi domin na tabbata ba zai yi rai ba bayan ya fāɗi. Na kuma cire kambin da yake kansa da ƙarau da yake a dantsensa. Ga su, na kawo wa ubangijina.”

11. Sai Dawuda ya yayyage tufafinsa. Dukan mutanen da suke tare da shi kuma suka yayyage nasu.

12. Suka yi makoki, da kuka, da azumi har maraice saboda Saul, da Jonatan ɗansa, da mutanen Ubangiji, da gidan Isra'ila domin an Karkashe su a yaƙi.

13. Dawuda ya ce wa mutumin nan da ya kawo labarin, “Daga ina ka zo?”Sai ya ce masa, “Ai, ni ɗan wani baƙo ne, Ba'amaleke.”

14. Dawuda ya ce, “Me ya sa ba ka ji tsoro ka miƙa hannunka, ka hallaka wanda Ubangiji ya keɓe ba?”

15. Sai Dawuda ya kira ɗaya daga cikin samarin, ya ce masa, “Ka kashe shi.” Ya dai buge shi, ya mutu.

16. Dawuda kuwa ya ce, “Alhakin jininka yana bisa kanka tun da yake da bakinka ka ce, ‘Ni ne na kashe wanda Ubangiji ya keɓe.’ ”

17. Sai Dawuda ya raira waƙar makoki domin Saul da Jonatan, ɗansa.

18. Ya umarta a koya wa mutanen Yahuza wannan waƙa. (An rubuta ta a littafin Yashar.)

19. “An kashe darajarki, ya Isra'ila, a kan tuddanki!Jarumawan sojojinmu sun fāɗi!

20. Kada a ba da labarin a Gat,Ko a titin Ashkelon.Kada ku sa matan Filistiyawa su yi murna,Kada ku sa 'yan matan arna su yi farin ciki.

Karanta cikakken babi 2 Sam 1