Tsohon Alkawari

Sabon Wasiya

1 Tar 7:29-35 Littafi Mai Tsarki (HAU)

29. Zuriyar Manassa sun mallaki Bet-sheyan, da Ta'anak, da Magiddo, da Dor duk da garuruwan da suke kewaye da su. A nan ne zuriyar Yusufu, ɗan Isra'ila, suka zauna.

30. 'Ya'yan Ashiru, maza, su ne Yimna, da Yishuwa, da Yishwi, da Beriya, da 'yar'uwarsu Sera.

31. 'Ya'yan Beriya, maza, su ne Eber, da Malkiyel wanda ya kafa garin Birzayit.

32. Eber shi ne mahaifin Yaflet, da Shemer, da Helem, da 'yar'uwarsu Shuwa.

33. 'Ya'yan Yaflet, maza, su ne Fasak, da Bimhal, da Ashewat.

34. 'Ya'yan Shemer maza, su ne Ahi, da Roga, da Yehubba, da Aram.

35. 'Ya'ya maza na ɗan'uwansa Helem, su ne Zofa, da Imna, da Sheles da Amal.

Karanta cikakken babi 1 Tar 7