Tsohon Alkawari

Sabon Wasiya

1 Tar 7:19-29 Littafi Mai Tsarki (HAU)

19. 'Ya'yan Shemida, maza, su ne Ahiyan, da Shekem, da Liki, da Aniyam.

20. 'Ya'yan Ifraimu, maza, daga tsara zuwa tsara, su ne Shutela, da Bered, da Tahat, da Eleyada, da Tahat,

21. da Zabad, da Shutela, da Ezer, da Eleyad waɗanda mutanen Gat, haifaffun ƙasar, suka kashe sa'ad da suka kai hari don su kwashe dabbobinsu.

22. Sai mahaifinsu, Ifraimu, ya yi ta makoki kwanaki da yawa. 'Yan'uwansu kuwa suka zo don su yi masa ta'aziyya.

23. Sa'an nan ya shiga wurin matarsa, ta kuwa sami juna biyu, ta haifi ɗa, ya raɗa masa suna Beriya saboda masifar da ta auko wa gidansa.

24. 'Yarsa kuma ita ce Sheyera, wadda ta gina garin Bet-horon na kwari da na tudu, ta kuma gina Uzzen-sheyera.

25. Waɗansu zuriyarsa bi da bi, su ne Refa, da Reshe, da Tela, da Tahan,

26. da Ladan, da Ammihud, da Elishama,

27. da Nun, da Joshuwa.

28. Mallakarsu da wuraren zamansu, su ne Betel duk da garuruwanta, da Nayaran wajen gabas, da Gezer wajen yamma duk da garuruwanta, da Shekem duk da garuruwanta, har zuwa Ayya duk da garuruwanta.

29. Zuriyar Manassa sun mallaki Bet-sheyan, da Ta'anak, da Magiddo, da Dor duk da garuruwan da suke kewaye da su. A nan ne zuriyar Yusufu, ɗan Isra'ila, suka zauna.

Karanta cikakken babi 1 Tar 7