Tsohon Alkawari

Sabon Wasiya

1 Tar 6:44-56 Littafi Mai Tsarki (HAU)

44. Etan na zuriyar Merari, shi ne shugaban ƙungiyar mawaƙa ta uku, asalinsa shi ɗan Kishi ne, ɗan Abdi, ɗan Malluki,

45. ɗan Hashabiya, ɗan Amaziya, ɗan Hilkiya,

46. ɗan Amzi, ɗan Bani, ɗan Shemer,

47. ɗan Mali, ɗan Mushi, ɗan Merari, ɗan Lawi.

48. Aka sa 'yan'uwansu, Lawiyawa, su yi dukan hidimomi a cikin Haikalin Ubangiji.

49. Amma Haruna da 'ya'yansa maza suka miƙa hadayu a kan bagaden hadaya ta ƙonawa, da kan bagaden ƙona turare, domin dukan aikin Wuri Mafi Tsarki, da kuma yin kafara domin Isra'ila bisa ga dukan abin da Musa, bawan Allah, ya umarta.

50. Waɗannan su ne zuriyar Haruna, maza, bi da bi, Ele'azara, da Finehas, da Abishuwa,

51. da Bukki, da Uzzi, da Zerahiya,

52. da Merayot, da Amariya, da Ahitub,

53. da Zadok da Ahimawaz.

54. Ga wuraren da aka ba zuriyar Haruna, na iyalin Kohat. Sun karɓi rabo na farko a ƙasar.

55. Rabonsu ya haɗu da Hebron ta yankin ƙasar Yahuza, da makiyayar da suke kewaye da ita.

56. Amma an ba Kalibu ɗan Yefunne saurukan birnin, tare da ƙauyukansa.

Karanta cikakken babi 1 Tar 6