Tsohon Alkawari

Sabon Wasiya

1 Tar 6:31-42 Littafi Mai Tsarki (HAU)

31. Waɗannan su ne waɗanda Dawuda ya sa su su zama mawaƙa a Haikalin Ubangiji, sa'ad da aka kawo akwatin alkawari a cikin Haikalin.

32. Suka yi ta raira waƙoƙi a gaban wurin zama na alfarwa ta taruwa tun kafin Sulemanu ya gina Haikalin Ubangiji a Urushalima. Suka yi hidima bisa ga matsayinsu ta yadda aka tsara.

33. Waɗannan su ne waɗanda suka yi ta raira waƙoƙin, su da 'ya'yansu maza.Daga iyalin Kohat, Heman shi ne shugaban ƙungiyar farko ta mawaƙa, shi ɗan Yowel ne, ɗan Sama'ila,

34. ɗan Elkana, ɗan Yeroham, ɗan Eliyab, ɗan Mahat,

35. ɗan Zafai, ɗan Elkana, ɗan Mahat, ɗan Amasai,

36. ɗan Elkana, ɗan Shawul, ɗan Azariya, ɗan Uriyel,

37. ɗan Tahat, ɗan Assir, ɗan Ebiyasaf, ɗan Kora,

38. ɗan Izhara, ɗan Kohat, ɗan Lawi, ɗan Isra'ila.

39. Asaf kuma shi ne shugaban ƙungiyar mawaƙa ta biyu. Shi ɗan Berikiya ne, ɗan Shimeya,

40. ɗan Maikel, ɗan Ba'aseya, ɗan Malkiya,

41. ɗan Yewaterai, ɗan Zera, ɗan Iddo,

42. ɗan Yowa, ɗan Zimma, ɗan Shimai,

Karanta cikakken babi 1 Tar 6