Tsohon Alkawari

Sabon Wasiya

1 Tar 4:9-15 Littafi Mai Tsarki (HAU)

9. Yabez ya fi sauran 'yan'uwansa kwarjini saboda haka mahaifiyarsa ta sa masa suna Yabez, wato da wahala ta haife shi.

10. Yabez ya roƙi Allah na Isra'ila, ya ce, “Ka sa mini albarka, ka faɗaɗa kan iyakata, hannunka kuma ya kasance tare da ni, ka kuma kiyaye ni daga abin da zai cuce ni.” Allah kuwa ya biya masa bukatarsa.

11. Kalibu ɗan'uwan Shuwa, shi ne mahaifin Mehir wanda ya haifi Eshton.

12. Eshton kuwa shi ne ya haifi Bet-rafa, da Faseya, da Tehinna wanda ya kafa birnin Ir-nahash, zuriyar waɗannan mutane kuwa su suka zauna a Reka.

13. 'Ya'yan Kenaz, maza, su ne Otniyel da Seraiya. Yana kuma da waɗansu 'ya'ya maza, su ne Hatata da Meyonotai.

14. Meyonotai kuwa shi ne mahaifin Ofra.Seraiya shi ne ya haifi Yowab, Yowab ya kafa kwarin Ge-harashim, saboda su masu sana'a ne.

15. 'Ya'yan Kalibu, maza, ɗan Yefunne, su ne Airu, da Ila, da Na'am. Ila shi ya haifi Kenaz.

Karanta cikakken babi 1 Tar 4