Tsohon Alkawari

Sabon Wasiya

1 Tar 3:1-3-9 Littafi Mai Tsarki (HAU)

1-3. Waɗannan su ne 'ya'yan Dawuda, maza, waɗanda aka haifa masa a Hebron.Amnon wanda Ahinowam Bayezreyeliya ta haifa masa.Kileyab wanda Abigail Bakarmeliya ta haifa masa.Absalom ɗan Ma'aka 'yar Talmai, Sarkin Geshur.Adonaija ɗan Haggit.Shefatiya wanda Abital ta haifa.Itireyam wanda Egla ta haifa.

4. Dukansu shida an haife su ne a Hebron inda ya yi sarauta shekara bakwai da wata shida.Ya yi sarauta a Urushalima shekara talatin da uku.

5. Waɗanda aka haifa masa a Urushalima, su ne Shimeya, da Shobab, da Natan, da Sulemanu, su huɗu ke nan waɗanda Bat-sheba 'yar Ammiyel ta haifa masa.

6. Yana da waɗansu 'ya'ya kuma, su ne Ibhar, da Elishuwa da Elifelet,

7. da Noga, da Nefeg, da Yafiya,

8. da Elishama, da Eliyada, da kuma Elifelet, su tara ke nan.

9. Waɗannan duka su ne 'ya'yan Dawuda, maza, banda 'ya'yan ƙwaraƙwarai. Tamar ita ce 'yar'uwarsu.

Karanta cikakken babi 1 Tar 3