Tsohon Alkawari

Sabon Wasiya

1 Tar 29:1-4 Littafi Mai Tsarki (HAU)

1. Sarki Dawuda fa ya yi magana da dukan taron, ya ce, “Ga shi, ɗana Sulemanu, wanda Allah ya zaɓa, shi dai saurayi ne tukuna, bai gogu da duniya ba tukuna, aikin kuwa babba ne, gama Haikali ba na mutum ba ne, amma na Ubangiji Allah ne.

2. A halin yanzu dai na riga na yi iyakacin ƙoƙarina, har na tanada waɗannan abubuwa saboda Haikalin Allahna, wato zinariya saboda kayayyakin zinariya, azurfa saboda kayayyakin azurfa, tagulla saboda kayayyakin tagulla, baƙin ƙarfe saboda kayayyakin baƙin ƙarfe, itace kuwa saboda kayayyakin itace, da duwatsu da yawa masu daraja, da masu launi iri iri.

3. Saboda kuma ƙaunar Haikalin Allahna da nake yi, shi ya sa na ba da zinariyata da azurfata domin Haikalin Allahna, banda wanda na riga na tanada saboda Haikali mai tsarki.

4. Na ba da zinariya tsantsa, talanti dubu uku (3,000), da azurfa tsantsa, talanti dubu bakwai (7,000), domin yin ado a bangon Haikalin,

Karanta cikakken babi 1 Tar 29