Tsohon Alkawari

Sabon Wasiya

1 Tar 28:1-5 Littafi Mai Tsarki (HAU)

1. Dawuda ya yi umarni a tara dukan shugabannin Isra'ila, da shugabannin kabilai, da shugabannin ƙungiyoyin da suke bauta wa sarki, da shugabannin dubu dubu, da na ɗari ɗari, da masu lura da dukan dukiya da dabbobin sarki, da na 'ya'yansa, da fādawa, da manyan sojoji, da jarumawa, a Urushalima.

2. Sarki Dawuda fa ya miƙe tsaye, ya ce, “Ku saurare ni, ku 'yan'uwana, da jama'ata. Na yi niyya a zuciyata in gina wa akwatin alkawari na Ubangiji wurin hutawa, da wurin zaman zatin Allah. Na riga na yi shiri domin ginin,

3. amma Allah bai yardar mini in yi da kaina ba, domin ni mayaƙi ne, na kuwa zubar da jini.

4. Duk da haka Ubangiji Allah na Isra'ila ya zaɓe ni da zuriyata daga cikin gidan mahaifina, in zama Sarkin Isra'ilawa har abada. Gama shi ya zaɓi Yahuza ya zama shugaba. Daga cikin gidan Yahuza kakana, da kuma daga cikin 'ya'yan mahaifina, maza, ya ji daɗina har ya naɗa ni sarkin dukan Isra'ila.

5. Daga cikin dukan 'ya'yana maza, (gama Ubangiji ya ba ni 'ya'ya maza da yawa), ya zaɓi ɗana Sulemanu ya hau gadon sarautar Isra'ila, abin mulkin Ubangiji.

Karanta cikakken babi 1 Tar 28