Tsohon Alkawari

Sabon Wasiya

1 Tar 27:2-15 Littafi Mai Tsarki (HAU)

Waɗannan su ne shugabanni don kowane wata.Wata na 1, Yashobeyam, ɗan Zabdiyel. (Shi daga dangin Feresa na kabilar Yahuza ne.)Wata na 2, Dodai, ɗan Ahowa. (Miklot yake bi masa a shugabancin.)Wata na 3, Benaiya, ɗan Yehoyada firist. Shugaba ne daga cikin sanannun nan “talatin.” (Ɗansa Ammizzabad ya gāje shi a shugabancin ƙungiya.)Wata na 4, Asahel, ƙanen Yowab. (Ɗansa Zabadiya ya gāje shi.)Wata na 5, Shimeya, daga zuriyar Izhara.Wata na 6, Aira, ɗan Ikkesha, daga Tekowa.Wata na 7, Helez, mutumin Ifraimu, daga Felet.Wata na 8, Sibbekai, daga garin Husha. (Shi daga dangin Zera ne, na kabilar Yahuza.)Wata na 9, Abiyezer, daga Anatot na kabilar Biliyaminu.Wata na 10, Maharai, daga Netofa. (Shi ma daga dangin Zera ya fito.)Wata na 11, Benaiya, daga Firaton na kabilar Ifraimu.Wata na 12, Heled, daga Netofa. (Shi daga zuriyar Otniyel ne.)

Karanta cikakken babi 1 Tar 27

gani 1 Tar 27:2-15 a cikin mahallin