Tsohon Alkawari

Sabon Wasiya

1 Tar 24:1-23 Littafi Mai Tsarki (HAU)

1. Ga yadda 'ya'yan Haruna, maza, suka karkasu. 'Ya'yan Haruna, maza, su ne Nadab, da Abihu, da Ele'azara, da Itamar.

2. Amma Nadab da Abihu sun riga mahaifinsu mutuwa, ba su kuma da 'ya'ya. Saboda haka Ele'azara da Itamar suka shiga aikin firistoci.

3. Sai Dawuda da Zadok daga zuriyar Ele'azara, da Ahimelek daga zuriyar Itamar suka karkasa su bisa ga ƙayyadaddun lokatansu na yin aiki.

4. Tun da yake akwai manyan mutane da yawa a zuriyar Ele'azara fiye da zuriyar Itamar, sai suka karkasa su haka, shugabannin gidajen kakannin zuriyar Ele'azara mutum goma sha shida, na zuriyar Itamar kuwa su takwas, bisa ga gidajen kakanninsu.

5. Da haka aka karkasa su ta hanyar kuri'a gama akwai ma'aikatan Wuri Mai Tsarki da kuma ma'aikata na Allah daga zuriyar Ele'azara da zuriyar Itamar.

6. Shemaiya, ɗan Netanel marubuci, Balawe, ya rubuta su a gaban sarki da shugabanni, da Zadok firist, da Ahimelek ɗan Abiyata, da shugabannin gidajen kakannin firistoci, da Lawiyawa. Aka ɗauki gida guda daga gidajen kakannin Ele'azara, aka kuma ɗauki ɗaya daga gidajen kakannin Itamar.

7-18. Ga yadda aka shirya ƙungiyoyin iyali ashirin da huɗu su sami aikinsu, 1) Yehoyarib, 2) Yedaiya, 3) Harim, 4) Seyorim, 5) Malkiya, 6) Mijamin, 7) Hakkoz, 8) Abaija, 9) Yeshuwa, 10) Shekaniya, 11) Eliyashib, 12) Yakim, 13) Huffa, 14) Yeshebeyab, 15) Bilga, 16) Immer, 17) Hezir, 18) Haffizzez, 19) Fetahiya, 20) Yehezkel, 21) Yakin, 22) Gamul, 23) Delaiya, 24) Ma'aziya.

19. Waɗannan suna da aikin da aka ba su na hidimar Haikalin Ubangiji bisa ga ka'idar da kakansu Haruna ya kafa musu, kamar yadda Ubangiji Allah na Isra'ila ya umarce shi.

20. Sauran 'ya'yan Lawi, maza, na wajen Amram, shi ne Shebuwel.Na wajen Shebuwel, shi ne Yedaiya.

21. Na wajen Rehabiya, shi ne Isshiya,

22. Na wajen Izhara, shi ne Shelomit, na wajen Shelomit, shi ne Yahat.

23. Na wajen Hebron, su ne Yeriya na fari, da Amariya, da Yahaziyel, da Yekameyam.

Karanta cikakken babi 1 Tar 24