Tsohon Alkawari

Sabon Wasiya

1 Tar 23:2-10 Littafi Mai Tsarki (HAU)

2. Dawuda kuwa ya tattara dukan shugabannin Isra'ila, da firistoci, da Lawiyawa.

3. Aka ƙidaya Lawiyawa maza tun daga mai shekara talatin har sama, jimillarsu dubu talatin da dubu takwas (38,000).

4. Sai Dawuda ya ce dubu ashirin da dubu huɗu (24,000) daga cikinsu za su yi hidimar Haikalin Ubangiji, dubu shida (6,000) kuma su zama manyan ma'aikata da alƙalai,

5. dubu huɗu (4,000) su zama matsaran ƙofofi, dubu huɗu (4,000) kuma za su zama masu raira yabbai ga Ubangiji da kayayyakin bushe-bushe da na kaɗe-kaɗe waɗanda ya yi.

6. Dawuda kuwa ya kasa su kashi kashi bisa ga 'ya'yan Lawi maza, wato Gershon, da Kohat, da Merari.

7. 'Ya'yan Gershon maza, su ne Libni da Shimai.

8. 'Ya'yan Libni, maza, su ne Yehiyel, shi ne babba, da Zetam, da Yowel, su uku.

9. 'Ya'yan Shimai, maza kuwa, su ne Shelomit, da Heziyel, da Haran, su uku. Waɗannan su ne shugabannin gidajen kakanninsu, Libni.

10. 'Ya'yan Shimai, maza, su ne Yahat, da Zaina, da Yewush, da Beriya. 'Ya'yan Shimai, maza, ke nan, su huɗu.

Karanta cikakken babi 1 Tar 23