Tsohon Alkawari

Sabon Wasiya

1 Tar 23:11-19 Littafi Mai Tsarki (HAU)

11. Yahat shi ne babba, Zaina shi ne na biyu, amma Yewush, da Beriya ba su da 'ya'ya da yawa, saboda haka ana lasafta su a haɗe gida ɗaya.

12. 'Ya'yan Kohat, maza, su ne Amram, da Izhara, da Hebron, da Uzziyel, su huɗu ke nan.

13. 'Ya'yan Amram, maza, su ne Haruna, da Musa. Aka keɓe Haruna domin ya tsarkake abubuwa mafi tsarki, domin shi da 'ya'yansa za su ƙone turare a gaban Ubangiji, su yi masa hidima, su riƙa sa albarka da sunansa har abada.

14. Amma 'ya'yan Musa mutumin Allah, an lasafta su tare da kabilar Lawi.

15. 'Ya'yan Musa, maza, ke nan, Gershom da Eliyezer.

16. Ɗan Gershom babba shi ne Shebuwel.

17. Ɗan Eliyezer shi ne Rehabiya, shugaba, shi Eliyezer ba shi da waɗansu 'ya'ya, amma Rehabiya yana da 'ya'ya da yawa.

18. Ɗan Izhara shi ne Shelomit, shugaba.

19. 'Ya'yan Hebron, maza, su ne Yeriya, shi ne babba, da Amariya na biyu, da Yahaziyel na uku, da kuma Yekameyam na huɗu.

Karanta cikakken babi 1 Tar 23