Tsohon Alkawari

Sabon Wasiya

1 Tar 16:8-16 Littafi Mai Tsarki (HAU)

8. Ku yi godiya ga Ubangiji, ku yi shelar girmansa,Ku sanar wa sauran al'umma abubuwan da ya yi!

9. Ku raira masa waƙa, ku raira yabo gare shi,Ku faɗi dukan abubuwa masu banmamaki da ya yi!

10. Ku yi murna saboda mu nasa ne,Ku yi murna dukanku da kuke bauta wa Ubangiji!

11. Ku je wurin Ubangiji neman taimako,Ku tsaya a gabansa koyaushe.

12. Ku tuna da mu'ujizansa masu girma, masu banmamaki,Ku tuna kuma da hukuntai waɗanda ya yanke.

13. Ya ku zuriyar bawansa Ibrahim,Ya ku zuriyar zaɓaɓɓensa Yakubu.

14. Shi Ubangiji, shi ne Allahnmu,Umarnansa domin dukan duniya ne.

15. Zai cika alkawarinsa har abada,Alkawaransa kuma don dubban zamanai,

16. Yarjejeniyar da ya yi da Ibrahim,Da alkawarin da ya yi wa Ishaku.

Karanta cikakken babi 1 Tar 16