Tsohon Alkawari

Sabon Wasiya

1 Tar 16:38-43 Littafi Mai Tsarki (HAU)

38. Akwai kuma masu tsaron ƙofofi, wato Obed-edom ɗan Yedutun tare da 'yan'uwansa, su sittin da takwas, da Hosa.

39. Sai ya bar Zadok firist da 'yan'uwansa firistoci a wurin zama na Ubangiji a tudun da yake a Gibeyon.

40. Kowace safiya da maraice suna miƙa hadayu na ƙonawa ga Ubangiji a bisa bagaden ƙona hadaya, kamar yadda aka rubuta a dokokin Ubangiji, waɗanda ya ba Isra'ilawa.

41. Tare da su kuma akwai Heman, da Yedutun, da sauran waɗanda aka zaɓa musamman domin su yi godiya ga Ubangiji saboda madawwamiyar ƙaunarsa.

42. Heman da Yedutun suna lura da ƙaho, da kuge, da sauran kayan bushe-bushe da na kaɗe-kaɗe, waɗanda ake amfani da su lokacin raira waƙoƙin yabo ga Allah. 'Ya'yan Yedutun, maza, su aka ba aikin tsaron ƙofa.

43. Sa'an nan dukan jama'a suka watse, kowa ya koma gidansa, Dawuda kuma ya koma gidansa, ya sa wa iyalinsa albarka.

Karanta cikakken babi 1 Tar 16