Tsohon Alkawari

Sabon Wasiya

1 Tar 16:19-26 Littafi Mai Tsarki (HAU)

19. Jama'ar Ubangiji kima ne,Baƙi ne kuwa a ƙasar.

20. Suka yi ta yawo daga ƙasa zuwa ƙasa,Daga wannan mulki zuwa wancan.

21. Amma bai yarda kowa ya zalunce su ba,Ya tsauta wa sarakuna da yawa saboda su.

22. Ya ce, “Kada ku taɓa bayina, zaɓaɓɓu,Kada ku cuci annabawana!”

23. Ku raira waƙa ga Ubangiji, ku dukan duniya,Ku yi shelar albishir na ceton da ya yi mana kowace rana.

24. Ku yi shelar ɗaukakarsa ga al'ummai,Da ayyukansa masu girma ga dukan mutane,

25. Ubangiji da girma yake, wajibi ne mu yabe shi,Dole mu yi tsoronsa fiye da dukan alloli.

26. Gama allolin dukan sauran al'umma gumaka ne,Amma Ubangiji shi ne ya halitta sammai.

Karanta cikakken babi 1 Tar 16