Tsohon Alkawari

Sabon Wasiya

1 Tar 16:1-14 Littafi Mai Tsarki (HAU)

1. Suka fa shigo da akwatin alkawarin Allah, suka ajiye shi a cikin alfarwar da Dawuda ya kafa masa, suka miƙa hadayu na ƙonawa da na salama a gaban Allah.

2. Da Dawuda ya gama miƙa hadayar ƙonawa da ta salama, sai ya sa wa jama'a albarka da sunan Ubangiji.

3. Ya kuma rarraba wa Isra'ilawa mata da maza, gurasa, da gunduwar nama, da kauɗar zabibi.

4. Ya kuma sa waɗansu Lawiyawa su yi hidima a gaban akwatin alkawarin Ubangiji, su ɗaukaka Ubangiji Allah na Isra'ila, su gode masa, su kuma yabe shi.

5. Asaf shi ne shugaba, na biye da shi su ne Zakariya da Aziyel, da Shemiramot, da Yehiyel, da Mattitiya, da Eliyab, da Benaiya, da Obed-edom, da Yehiyel, waɗanda za su kaɗa molaye da garayu. Asaf kuwa shi ne mai kaɗa kuge.

6. Benaiya da Yahaziyel firistoci, su ne za su riƙa busa ƙaho a gaban akwatin alkawarin Allah.

7. A wannan lokaci ne Dawuda ya fara sa Asaf da 'yan'uwansa su riƙa raira waƙoƙin yabo ga Ubangiji.

8. Ku yi godiya ga Ubangiji, ku yi shelar girmansa,Ku sanar wa sauran al'umma abubuwan da ya yi!

9. Ku raira masa waƙa, ku raira yabo gare shi,Ku faɗi dukan abubuwa masu banmamaki da ya yi!

10. Ku yi murna saboda mu nasa ne,Ku yi murna dukanku da kuke bauta wa Ubangiji!

11. Ku je wurin Ubangiji neman taimako,Ku tsaya a gabansa koyaushe.

12. Ku tuna da mu'ujizansa masu girma, masu banmamaki,Ku tuna kuma da hukuntai waɗanda ya yanke.

13. Ya ku zuriyar bawansa Ibrahim,Ya ku zuriyar zaɓaɓɓensa Yakubu.

14. Shi Ubangiji, shi ne Allahnmu,Umarnansa domin dukan duniya ne.

Karanta cikakken babi 1 Tar 16