Tsohon Alkawari

Sabon Wasiya

1 Tar 15:1-4 Littafi Mai Tsarki (HAU)

1. Dawuda kuwa ya gina wa kansa gidaje a birninsa, ya kuma kafa alfarwa domin akwatin alkawari na Allah.

2. Sai Dawuda ya ce, “Kada wani ya ɗauki akwatin alkawari na Allah sai Lawiyawa kaɗai, gama su ne Ubangiji ya zaɓa domin su riƙa ɗaukar akwatin alkawarin Ubangiji, su kuma yi masa hidima har abada.”

3. Saboda haka Dawuda ya tattara Isra'ilawa duka a Urushalima don a kawo akwatin alkawarin Ubangiji a wurinsa, inda aka riga aka shirya masa.

4. Dawuda kuma ya tattara zuriyar Haruna a wuri ɗaya, tare kuma da Lawiyawa.

Karanta cikakken babi 1 Tar 15