Tsohon Alkawari

Sabon Wasiya

1 Tar 14:11-17 Littafi Mai Tsarki (HAU)

11. Sai suka haura zuwa Ba'al-ferazim, Dawuda kuwa ya ci su da yaƙi a wurin. Sai ya ce, “Allah ya raraki maƙiyana ta hannuna, kamar yadda ruwa yakan rarake ƙasa.” Don haka aka sa wa wurin suna Ba'al-ferazim.

12. Filistiyawa suka gudu suka bar gumakansu a wurin. Dawuda kuwa ya yi umarni, aka ƙone su duka.

13. Filistiyawa kuma suka sāke kawo yaƙi a kwarin.

14. Dawuda ya sāke yin roƙo ga Allah, Allah kuwa ya ce masa, “Kada ka hau zuwa wurinsu, ka kewaye ka ɓullo musu ta baya daura da itatuwan tsamiya.

15. Sa'ad da ka ji motsi kamar na tafiyar sojoji a bisa itatuwan tsamiya, sai ka fita ka yi yaƙi, gama Allah ya wuce ta gabanka don ya bugi sojojin Filistiyawa.”

16. Dawuda fa ya yi daidai yadda Ubangiji ya umarce shi. Suka bugi sojojin Filistiyawa tun daga Geba har zuwa Gezer.

17. Sunan Dawuda kuma ya kai ko'ina cikin dukan ƙasashe. Ubangiji kuwa ya sa dukan al'ummai su ji tsoron Dawuda.

Karanta cikakken babi 1 Tar 14