Tsohon Alkawari

Sabon Wasiya

1 Tar 12:18-28 Littafi Mai Tsarki (HAU)

18. Ruhun Allah kuwa ya sauko a kan Amasa wanda daga baya ya zama shugaban talatin ɗin, sai ya ce,“Muna tare da kai, ya Dawuda ɗan Yesse!Allah ya ba ka nasara tare da waɗanda suke tare da kai!Allah yana wajenka!”Sa'an nan Dawuda ya marabce su, ya maishe su shugabanni a sojojinsa.

19. Waɗansu sojoji daga Manassa, suka tafi wurin Dawuda sa'ad da yake fita tare da Filistiyawa don su yi yaƙi da Saul. Amma Dawuda bai tafi tare da su ba, domin sarakunan Filistiyawa sun yi shawara, suka sallame shi, don kada ya juya musu gindin baka, ya nemi sulhu a wurin shugabansu Saul, da kawunansu.

20. Sa'ad da yake komawa Ziklag sai sojojin Manassa suka zo wurinsa, wato su Adana, da Yozabad, da Yediyayel, da Maikel, da Yozabad, da Elihu, da Zilletai. A sojojin kabilar Manassa, waɗannan shugabannin sojoji ne na dubu dubu.

21. Suka kuwa taimaki Dawuda sa'ad da mahara take tasar masa, gama dukansu jarumawa ne sosai, su kuma shugabannin sojoji ne.

22. Kowace rana mutane suna ta zuwa wurin Dawuda don su taimake shi, har suka zama babbar runduna.

23. Horarrun sojoji da yawa suka haɗa kai da sojojin Dawuda a Hebron domin su taimaki Dawuda da yaƙi, su mai da shi sarki maimakon Saul, kamar yadda Ubangiji ya alkawarta. Ga yadda yawansu yake.

24. Mutanen Yahuza waɗanda suke riƙe da garkuwoyi da māsu don yaƙi, mutum dubu shida da ɗari takwas (6,800).

25. Na kabilar Saminu jarumawa mayaƙa mutum dubu bakwai da ɗari (7,100).

26. Na kabilar Lawi akwai mutum dubu huɗu da ɗari shida (4,600).

27. Akwai kuma Yehoyada wanda shi ne shugaban gidan Haruna, yana da mutum dubu uku da ɗari bakwai (3,700).

28. Na dangin Zadok wanda yake jarumi, saurayi, akwai shugabannin sojoji ashirin da biyu.

Karanta cikakken babi 1 Tar 12