Tsohon Alkawari

Sabon Wasiya

1 Tar 12:1-8 Littafi Mai Tsarki (HAU)

1. Mutane da yawa suka haɗa kai da Dawuda lokacin da yake a Ziklag, sa'ad da yake a takure saboda Saul ɗan Kish. Su ma suna cikin manyan jarumawan da suka taimake shi yaƙi. Dukansu gwanayen sojoji ne, suna iya su harba kibiya, ko su yi jifa da majajjawa da hannun dama ko da na hagu.

2. Su daga kabilar Biliyaminu ne, dangin Saul.

3-7. Waɗannan su ne shugabannin sojoji,Ahiyezer, da Yowash, 'ya'yan Shemaiya, maza, daga GibeyaYeziyel, da Felet, 'ya'yan Azmawet, mazaBeraka, da Yehu daga AnatotIsmaya daga Gibeyon babban jarumine a cikin jarumawan nan talatin,yana daga cikin shugabanninjarumawa talatin ɗinIrmiya, da YahaziyelYohenan, da Yozabad daga GederaEluzai, da Yerimot, da Be'aliyaShemariya, da Shefatiya daga HarifElkana, da Isshiya, da AzarelYowezer, da Yashobeyam daga iyalinKoraYowela, da Zabadiya 'ya'ya maza naYeroham na Gedor

8. Waɗannan su ne sunayen shahararru, ƙwararrun mayaƙa daga kabilar Gad, waɗanda suka haɗa kai da sojojin Dawuda, sa'ad da yake a kagara a hamada. Su gwanayen yaƙi da garkuwa da mashi ne. Fuskokinsu kamar na zakoki, saurinsu kamar bareyi a kan dutse.

Karanta cikakken babi 1 Tar 12