Tsohon Alkawari

Sabon Wasiya

1 Sar 7:30-38 Littafi Mai Tsarki (HAU)

30. Kowane dakali yana da ƙafa huɗu na tagulla kamar na karusa, da sandunan tagulla don sa kwatarniya. A kusurwoyin akwai abubuwa na zubi don tallabar kwatarniya. An zana furanni a kowane gefensu.

31. Bakinsa daga cikin dajiyar ya yi sama kamu guda. Bakin da'ira ne kamar fasalin gammo, kamu ɗaya da rabi. Akwai zāne-zāne a bakin. Sassan murabba'i ne, ba da'ira ba.

32. Ƙafafu huɗu ɗin, suna ƙarƙashin sassan. Sandunan ƙafafun a haɗe suke da dakalan. Tsayin kowace ƙafa kuwa kamu ɗaya da rabi ne.

33. Ƙafafun suna kama da ƙafafun karusa. Sandunan ƙafafun, da gyaffansu, da kome na ƙafafun duka na zubi ne.

34. Akwai ginshiƙi huɗu daga ƙarƙashin kowane dakali. Ginshiƙan suna haɗe da dakalan.

35. Akwai wani abu kamar gammo mai tsayi rabin kamu a kan dakalin. Ginshiƙan kuma da sassan a haɗe suke da dakalin.

36. Ya zana siffofin kerubobi, da na zakoki, da na itatuwan dabino a jikin ginshiƙan da sassan a duk inda ya ga akwai fili. Ya kuma zana furanni kewaye da su.

37. Haka aka yi dakalai, dukansu iri ɗaya ne, girmansu da fasalinsu kuma iri ɗaya ne.

38. Ya kuma yi daruna na tagulla guda goma. Kowane daro yana cin misalin garwa tamanin. Kowane daro kamu huɗu ne. Kowane dakali yana da daro ɗaya.

Karanta cikakken babi 1 Sar 7