Tsohon Alkawari

Sabon Wasiya

1 Sar 7:14-33 Littafi Mai Tsarki (HAU)

14. Shi ɗan wata mata ne daga kabilar Naftali wadda mijinta ya rasu. Huram mutumin Taya ne, maƙerin tagulla. Yana da hikima, da fahimi, da fasaha na iya yin kowane irin aiki da tagulla. Ya kuwa amsa kiran sarki Sulemanu, ya zo ya yi masa dukan aikinsa.

15. Ya kuwa yi ginshiƙi biyu na zubi da tagulla. Kowane ginshiƙi tsayinsa kamu goma sha takwas ne, da guru mai kamu goma sha biyu kewaye da shi.

16. Ya kuma yi dajiya biyu ta zubi da tagulla don a sa a kan ginshiƙan. Tsayin kowace dajiya kamu biyar ne.

17. Ya yi wa kowace dajiya da take kan ginshiƙan ragogi da tukakkun sarƙoƙi. Kowace dajiya tana da guda bakwai.

18. Ta haka ya yi ginshiƙai jeri biyu kewaye da raga don rufe dajiya wadda take da siffofin rumman, haka kuma ya yi wa ɗaya dajiyar.

19. Dajiyar da take kan ginshiƙai na cikin shirayin an yi su da fasalin bi-rana kamu huɗu huɗu.

20. Dajiyar tana kan ginshiƙan nan biyu kusa da wani abu mai kama da gammo, wanda yake kusa da ragar. Akwai jeri biyu na siffofin rumman guda ɗari biyu a kewaye da dajiyar.

21. Ya kafa ginshiƙan a shirayin Haikalin. Ya kafa ginshiƙi ɗaya a wajen dama, ya sa masa suna, Yakin, wato Allah ya kafa. Ya kafa ɗaya ginshiƙin a wajen hagu, ya sa masa suna Bo'aza, wato da ƙarfin Allah.

22. A bisa kawunan ginshiƙan akwai dajiya masu fasalin bi-rana. Haka aka gama aikin ginshiƙan.

23. Huram kuma ya yi kewayayyiyar babbar kwatarniya ta zubi da tagulla. Faɗinta kamu goma ne, tsayinta kuwa kamu biyar, da'irarta kuma kamu talatin ne.

24. Akwai goruna kewaye da gefensa. Gora goma a kowane kamu ɗaya. Suka kewaye kwatarniya. Gorunan jeri biyu ne, an yi zubinsu haɗe da kwatarniyar.

25. Aka ɗora ta a kan siffofin bijimai goma sha biyu. Siffofin bijimai uku suna fuskantar gabas, uku kuma suna fuskantar yamma, uku suna fuskantar kudu, uku kuma suna fuskantar arewa. An ɗora kwatarniya a kansu. Gindinsu duka na wajen ciki.

26. Kaurin kwatarniya ya kai taƙin hannu guda. An yi gefenta kamar finjali, kamar kuma furen bi-rana. Takan ci garwa dubu biyu.

27. Ya kuma yi dakali goma da tagulla. Kowane dakali tsawonsa kamu huɗu, faɗinsa kuma kamu huɗu, tsayinsa kuwa kamu uku ne.

28. Yadda aka yi dakalan ke nan, dakalan suna da sassa, sassan kuma suna da mahaɗai.

29. Aka zana hotunan zakoki, da na bijimai, da na kerubobi a kan sassan. A kan mahaɗan kuma akwai gammo, aka zana hotunan furanni a ƙarƙashin zakokin da bijiman.

30. Kowane dakali yana da ƙafa huɗu na tagulla kamar na karusa, da sandunan tagulla don sa kwatarniya. A kusurwoyin akwai abubuwa na zubi don tallabar kwatarniya. An zana furanni a kowane gefensu.

31. Bakinsa daga cikin dajiyar ya yi sama kamu guda. Bakin da'ira ne kamar fasalin gammo, kamu ɗaya da rabi. Akwai zāne-zāne a bakin. Sassan murabba'i ne, ba da'ira ba.

32. Ƙafafu huɗu ɗin, suna ƙarƙashin sassan. Sandunan ƙafafun a haɗe suke da dakalan. Tsayin kowace ƙafa kuwa kamu ɗaya da rabi ne.

33. Ƙafafun suna kama da ƙafafun karusa. Sandunan ƙafafun, da gyaffansu, da kome na ƙafafun duka na zubi ne.

Karanta cikakken babi 1 Sar 7