Tsohon Alkawari

Sabon Wasiya

1 Sar 3:16-22 Littafi Mai Tsarki (HAU)

16. Wata rana waɗansu mata masu zaman kansu, su biyu, suka zo gaban sarki.

17. Sai ɗayar ta ce, “Ran sarki ya daɗe, ni da wannan mata a gida ɗaya muke zaune, sai na haifi ɗa namiji, ita kuwa tana nan a gidan.

18. Bayan kwana uku da haihuwata, ita ma sai ta haihu. Mu kaɗai ne, ba kowa tare da mu a gidan.

19. Ana nan sai ɗan wannan mata ya mutu da dare, domin ta kwanta a kansa.

20. Da tsakar daren sai ta tashi, ta ɗauke ɗana daga wurina, sa'ad da nake barci, ta kai shi gadonta, sa'an nan ta kwantar da mataccen ɗanta a wurina.

21. Sa'ad da na tashi da safe don in ba ɗana mama, sai ga shi, matacce. Da na duba sosai, sai na ga ba nawa ba ne, wanda na haifa.”

22. Amma ɗaya matar ta ce, “A'a, mai ran shi ne nawa, mataccen kuwa shi ne naki!”Sai ta fari ta ce, “A'a, mataccen shi ne naki, mai rai ne nawa!”Haka suka yi ta gardama a gaban sarki.

Karanta cikakken babi 1 Sar 3