Tsohon Alkawari

Sabon Wasiya

1 Sar 3:13-20 Littafi Mai Tsarki (HAU)

13. Na kuma ba ka abin da ba ka roƙa ba, wato wadata da girma. Domin haka a zamaninka ba za a sami wani sarki kamarka ba.

14. Idan za ka yi mini biyayya ka kuma kiyaye dokokina, da umarnaina kamar yadda tsohonka Dawuda ya yi, to, zan ba ka tsawon rai.”

15. Da Sulemanu ya farka, ashe, mafarki ne, Sa'an nan ya zo Urushalima, ya tafi ya tsaya a gaban akwatin alkawarin Ubangiji. Ya miƙa hadayu na ƙonawa, da hadayu na salama. Ya kuma yi wa dukan barorinsa biki.

16. Wata rana waɗansu mata masu zaman kansu, su biyu, suka zo gaban sarki.

17. Sai ɗayar ta ce, “Ran sarki ya daɗe, ni da wannan mata a gida ɗaya muke zaune, sai na haifi ɗa namiji, ita kuwa tana nan a gidan.

18. Bayan kwana uku da haihuwata, ita ma sai ta haihu. Mu kaɗai ne, ba kowa tare da mu a gidan.

19. Ana nan sai ɗan wannan mata ya mutu da dare, domin ta kwanta a kansa.

20. Da tsakar daren sai ta tashi, ta ɗauke ɗana daga wurina, sa'ad da nake barci, ta kai shi gadonta, sa'an nan ta kwantar da mataccen ɗanta a wurina.

Karanta cikakken babi 1 Sar 3