Tsohon Alkawari

Sabon Wasiya

1 Sar 3:10-18 Littafi Mai Tsarki (HAU)

10. Ubangiji kuwa ya ji daɗin abin da Sulemanu ya roƙa.

11. Ya kuma ce masa. “Da yake ka roƙi wannan, ba ka roƙar wa kanka yawan kwanaki, ko wadata ba, ko kuma ran maƙiyanka, amma ka roƙa a ba ka hikima yadda za ka mallaki jama'a,

12. to, zan yi maka yadda ka roƙa, zan ba ka zuciya ta hikima da ganewa har ba wanda ya kai kamarka, ba kuwa wanda zai kai kamarka.

13. Na kuma ba ka abin da ba ka roƙa ba, wato wadata da girma. Domin haka a zamaninka ba za a sami wani sarki kamarka ba.

14. Idan za ka yi mini biyayya ka kuma kiyaye dokokina, da umarnaina kamar yadda tsohonka Dawuda ya yi, to, zan ba ka tsawon rai.”

15. Da Sulemanu ya farka, ashe, mafarki ne, Sa'an nan ya zo Urushalima, ya tafi ya tsaya a gaban akwatin alkawarin Ubangiji. Ya miƙa hadayu na ƙonawa, da hadayu na salama. Ya kuma yi wa dukan barorinsa biki.

16. Wata rana waɗansu mata masu zaman kansu, su biyu, suka zo gaban sarki.

17. Sai ɗayar ta ce, “Ran sarki ya daɗe, ni da wannan mata a gida ɗaya muke zaune, sai na haifi ɗa namiji, ita kuwa tana nan a gidan.

18. Bayan kwana uku da haihuwata, ita ma sai ta haihu. Mu kaɗai ne, ba kowa tare da mu a gidan.

Karanta cikakken babi 1 Sar 3