Tsohon Alkawari

Sabon Wasiya

1 Sar 3:1-7 Littafi Mai Tsarki (HAU)

1. Sulemanu ya gama kai da Fir'auna, Sarkin Masar, ta wurin aure, domin ya auri 'yar Fir'auna, ya kawo ta birnin Dawuda kafin ya gama ginin gidan kansa, da Haikalin Ubangiji, da garun Urushalima.

2. Mutane suka yi ta miƙa hadayu a al'amudai dabam dabam, domin ba a gina haikalin Ubangiji ba tukuna.

3. Sulemanu ya ƙaunaci Ubangiji, ya yi tafiya bisa ga koyarwar tsohonsa, Dawuda, amma ya miƙa sadakoki da hadayu da yawa a al'amudai dabam dabam.

4. Sarki kuwa ya tafi Gibeyon don ya miƙa hadaya, gama a can ne akwai babban al'amudi. Ya miƙa hadayu na ƙonawa guda dubu a kan wannan bagade.

5. Ubangiji kuwa ya bayyana ga Sulemanu cikin mafarki a Gibeyon da dare, ya ce masa, “Ka roƙi abin da kake so in ba ka.”

6. Sulemanu ya amsa ya ce, “Kai ne kake nuna ƙauna mai girma a koyaushe ga bawanka Dawuda, tsohona,domin ya yi tafiya a gabanka da aminci, da adalci, da tawali'u. Kai kuwa ka tabbatar masa da wannan ƙauna mai girma, ka kuma ba shi ɗa wanda zai hau gadon sarautarsa a wannan rana.

7. Yanzu, ya Ubangiji Allahna, ka naɗa ni sarki, a matsayin Dawuda, tsohona, ko da yake ni yaro ne ƙarami, ban ƙware ba.

Karanta cikakken babi 1 Sar 3