Sarki kuwa ya tafi Gibeyon don ya miƙa hadaya, gama a can ne akwai babban al'amudi. Ya miƙa hadayu na ƙonawa guda dubu a kan wannan bagade.