Tsohon Alkawari

Sabon Wasiya

1 Sar 21:3-18 Littafi Mai Tsarki (HAU)

3. Amma Nabot ya ce wa Ahab, “Ubangiji ya sawwaƙa in ba ka gādon kakannina.”

4. Ahab ya koma gida da baƙin ciki da rai a ɓace saboda abin da Nabot Bayezreyele ya faɗa masa. Ahab ya kwanta a gadonsa, ya mai da fuskarsa bango ya ƙi cin abinci.

5. Yezebel, matarsa kuwa ta zo wurinsa, ta ce masa, “Me ya sa ka damu, ka ruɗe haka, har ka ƙi cin abinci?”

6. Ya ce mata, “Domin na yi magana da Nabot Bayezreyele, na ce ya sayar mini da gonar inabinsa, idan kuma yana so, sai in ba shi wata gonar inabi a maimakon tasa, amma ya ce ba zai ba ni gonar inabin ba.”

7. Yezebel, matarsa, ta ce masa, “Ba kai ne kake mulkin Isra'ila ba? Tashi, ka ci abinci, ka yi farin ciki, zan ba ka gonar inabin Nabot Bayezreyele.”

8. Sa'an nan ta rubuta wasiƙu da sunan Ahab, ta hatimce su da hatiminsa, sa'an nan ta aika da wasiƙun zuwa ga dattawa da fādawan da suke zaune a birnin tare da Nabot.

9. Ta rubuta a wasiƙun, “A yi shelar azumi, a sa Nabot a gaban jama'a.

10. A kuma sa 'yan iska guda biyu, su yi ta zarginsa, su riƙa cewa, ‘Nabot ya zagi Allah da sarki.’ Sa'an nan ku tafi da shi, ku jajjefe shi da duwatsu har ya mutu.”

11. Mutanen birnin kuwa, dattawa da fādawan da suke zaune a birnin suka yi yadda Yezebel ta sa su yi, kamar yadda aka rubuta a wasiƙun da ta aika musu.

12. Suka kuwa yi shelar azumi, suka sa Nabot a gaban jama'a. 'Yan iska guda biyu suka zauna kusa da shi, suka yi ta zarginsa a gaban jama'a, suna cewa, “Nabot ya zagi Allah da sarki.”

13. Sai suka fitar da shi daga cikin birni, suka jajjefe shi da duwatsu har ya mutu.

14. Sa'an nan suka aika wa Yezebel cewa, “An jajjefi Nabot, ya mutu.”

15. Nan da nan da Yezebel ta ji an jajjefi Nabot har ya mutu, sai ta ce wa Ahab, “Tashi, ka mallaki gonar inabin Nabot, wadda ya ƙi sayar maka, gama Nabot ba shi da rai, ya mutu.”

16. Da Ahab ya ji Nabo ya mutu, sai ya tashi ya gangara zuwa gonar inabin Nabot Bayezreyele don ya mai da ta tasa.

17. Sa'an nan Ubangiji ya ce wa Iliya Batishbe,

18. “Tashi, ka tafi, ka sadu da Ahab, Sarkin Isra'ila, wanda yake a Samariya, ga shi can a gonar inabin Nabot inda ya tafi don ya mallake ta.

Karanta cikakken babi 1 Sar 21